Jammeh na fuskantar adawa mai karfi
December 1, 2016Talla
'Yan Gambiya dubu 880 ne aka tantance su don kada kuri'un su cikin al'ummar kasar sama da miliyan daya. Sai dai a wannan karon shugaba mai-ci Yahya Jammeh mai shekaru 51 da ke neman tazarce na fuskantar adawa mai karfi daga abokan takararsa Adama Barrow da kuma Mama Kandeh, da dukkanin su suka lashi takobin ganin bayan shugabancinsa na shekaru 22.
Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun gargadi hukumomi da su kare hakkin al'umma, kuma kada a tauye 'yancin fadin albarkascin baki. Amma tuni wasu rahotanni ke cewa an fara fuskantar tangarda da wasu kafofin sada zumunta a kasar.
Shugaba Yayah Jammeh ya dare karagar mulkin Gambiya ne a shekara ta 1994, kuma ya ba da tabbacin gudanar da zaben cikin lumana ba tare da damar ta da hargisti ba.