Jammeh zai kashe masu son sauke shi
January 6, 2015Talla
Shugaba Jammeh ya ce wadanda suka yi irin wannan yunkuri a 2006 da 2009 an bukaci da ya yafe musu kuma ya yafe, amma a wannan karon zasu gane kurensu. Shugaban ya bayyana haka ne a fadarsa da ke Banjul babban birnin kasar gaban dimbin magoya bayansa, inda ya danganta masu son kifar da shi a matsayi sojan haya da basu kai kaso daya na 'yan kasar ba. Daga cikin wadanda ake zargi da kitsa juyin mulkin akwai wasu Amirkawa biyu 'yan asalin kasar ta Gambiya Cherno Njie, mai shekaru 57 a duniya da kuma Papa Faal mai shekaru 46 a duniya.
Mawallafa: Salissou Issa/Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohamadou Awal Balarabe