1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Bankwana da tashoshin nukiliya

Abdullahi Tanko Bala
April 15, 2023

Cikin 'yan sa'oi masu zuwa za a rufe ragowar tashoshin makamashin nukiliya guda uku da suka rage a Jamus.

https://p.dw.com/p/4Q8Rv
Atomausstieg in Deutschland | Abschaltfest AKW Neckarwestheim
Hoto: Stefan Puchner/dpa/picture alliance

Yayin da wasu 'yan siyasar suke maraba da rufe tashoshin nukiliyar wasu kuwa na yin kashedin cewa sabbin dabarun makamashi da ake son koma wa garesu za su fi fitar da gurbataccen hayaki.

Tashoshin uku da ke jihohin Bavaria da Lower Saxony da kuma Baden Wüttenberg ana fatan kawo karshen ayyukansu da tsakar daren wannan rana ta Asabar bayan tsawon shekaru 60 ana amfani da su wajen samar da makamashi.

An jinkirta rufe tashoshin da 'yan watanni sabanin yadda aka tsara sakamakon takaddamar makamashi wanda yakin da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine ya haifar a bara.