Jamus: CDU ta lashe zabe a jihar Saarland
March 26, 2017Talla
Rahotanni sun nunar da cewa jam'iyyar ta CDU nada sama da kaso 40 cikin 100 na kuri'un da aka kada yayin da abokiyar hamayyarta ta Social Democrat (SPD) ke da sama da kaso 30 cikin 100 na kuri'un. Wannan dai na nuni da cewa akwai sauran aiki gagarumi a gaban jam'iyyar ta SPD, a fatan da take da shi na lashe zaben shugabancin gwamnati a Jamus din, bayan da ta tsayar da Martin Schulz a matsayin dan takararta da zai kalubalanci Merkel a zaben da za a gudanar a watan Satumba mai zuwa a kasar.