Jamus da Indiya zasu karfafa ƙawancen su
October 17, 2010Ƙasashen Indiya da Jamus waɗanda suka sami kujerun karɓa-karɓa a kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya a makon da ya gabata, za su ƙaddamar da wata tattaunawa daga gobe litinin domin neman sabbin hanyoyin gyare-gyare a Majalisar Ɗinkin Duniya, har da matsalar canjin yanayi da matakan tsaro, da ma dabarun yaƙi da ta'adanci. Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya isa babban birini Indiya, wato New-Delhi a yau, inda zai gana da Frime Minista Manmohan Singh da ministan harkokin wajen Indiya Mr Mallaiah Krishna.
Kafin tafiyan dai Westerwelle ya faɗa wa manema labaru a nan Jamus cewa India na da mahimmanci sosai ga Jamus ba don bunƙasar kasuwanni kaɗai ba, amma har da bunƙasa a fannin siyasa.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Umaru Aliyu