Jamus: Gaggauta matakai kan masu neman mafaka
December 23, 2016A cikin wata hira ta wayar tarho da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi da shugaban Tunisiya Beji Caid Essebsi, ta matsa kaimi wajen ganin an gaggauta tasa keyar 'yan Tunisiya da ake shirin komawa da su gida daga Jamus. Kokarin tasa keyar Anis Amri da ake zargi da kai harin kan wata kasuwar kirsimeti ta birnin Berlin a farkon wannan makon ya ci-tura saboda rashin samun hadin kai daga mahukuntan kasar Tunisiya. Tana mai cewa a shekarun baya-bayan nan gwamati ta dauki tsauraran matakai don tunkarar barazanar da ake fuskanta daga 'yan ta'adda.
"Jamus da Tunisiya sun karfafa hadin kai a fannin yaki da ta'addanci. Mun kuma samu ci-gaba mai ma'anan a bangaren tasa keyar 'yan Tunisiya da ba su da izinin zama a Jamus, wannan kuwa na da muhimmanci a gare mu. Na kuma fada wa Shugaban Tunisiya cewa wajibi ne mu gaggauta shirin komawa da 'yan kasarsa gida tare da kara yawan wadanda muke koran."
Shi ma a nashi bangaren Ministan shari'a Heiko Maas da takwaransa Ministan cikin gida Thomas de Maiziere, sun sanar da daukar matakan gaggawa bisa manufar mayar da bakin da ba su da takardun izinin zama a Jamus zuwa kasashensu. Ministan shari'ar ya ce za su shirya wata tattaunawa a cikin watan Janairu kan yadda za a gaggauta korar wadannan baki. Shi kuwa Ministan cikin gida Thomas de Maiziere cewa ya yi duk da nasarar kashe maharin na Berlin har yanzu Jamus na fuskantar barazanar ta'addanci.
"Godiya ta musamman ga 'yan sandan Italiya dangane da wannan namijin aiki da suka yi, sun nuna bajimta. Ina kuma taya takwaran aikina na Italiya murnar wannan nasarar da 'yan sandan kasar suka yi. Sai dai duk da haka barazanar ta'addanci a Jamus ba ta canja ba. Muna cikin shirin ko-takwana, jami'an tsaro na aiki tukuru kamar yadda kame-kamen da suka yi a kwanakin nan suka nunar."
Gaba dayan shugabannin siyasa na bangarorin jam'iyyu a Jamus sun yi maraba da labarin kashe Anis Amri a Italiya, suna masu yin kira ga kasar ta tsaurara dokokinta na bada mafakar siyasa. Shi dai matashin dan kasar Tunisiya ya fito ne daga yankin Kairouan daya daga cikin yankunan da suka fi talauci a Tunisiya, inji Moncef Slimi edita a sashen larbaci na DW kuma dan kasar Tunisiya.
"Yankin Kairouan na zama wani wuri mai tsarki a Tunisiya, yanki ne kuma da ke zama cibiyar 'yan Salafiyya, inda wata babbar kungiyar Islama ta Ansar Al-Sharia ta taba gudanar da babban taronta jim kadan bayan guguwar canji da ta kada a Tunisiya a 2011.
Sai dai a lokacin tuni Amri ya bar kasar ya doshi nahiyar Turai. Tun dai yana da shekaru 17 ya bar gida zuwa Italiya, inda ya nemi mafaka amma aka yi watsi da bukatunsa. Ya dai kasance mai son tada hankali, abinda ya kai ga yi masa daurin shekaru hudu a kurkuku. Daga bisani ya shigo nan Jamus inda a nan din ma ba a amimce da takardunsa na neman mafaka ba.