1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Kada a firgita da dawowar 'yan IS

Abdullahi Tanko Bala
November 14, 2019

Jamus ta bukaci jama'ar kasarta kada su firgita dangane da dawowar wasu 'yan IS wadanda Turkiyya ta tasa keyarsu zuwa gida.

https://p.dw.com/p/3T4ad
Syrien al-Hol camp IS-Angeghörige
Hoto: Getty Images/AFP/D. Souleiman

Mahukunta a birnin Berlin sun tabbatar wa jama'a cewa 'yan IS din da aka tasa keyarsu ba su da wani hadari ga tsaron kasa. Sai dai wasu manazarta na cewa ya kamata gwamnati ta gaggawa mayar da su da zarar sun shigo kasar.

A cikin wannan makon ne dai ministan cikin gida na kasar Turkiyya ya sanar da cewa kasar za ta fara tasa keyar 'yan IS din da ta kama domin mayar da su kasashensu.

Kawo yanzu babu wani sammaci na kama iyalan dan IS din Kanan B wanda bajamushe ne mai asali da kasar Iraqi, abin da ke nufin cewa idan ta sauka za ta wuce zuwa gidansu da ke jihar Lower Saxony amma bisa rakiya yan sanda.