Seehofer ya nemi tasu ta zo daya da Merkel
June 18, 2018Kalaman na shugabar gwamnatin ta Jamus na zuwa ne jim kadan bayan da ministan cikin gida na kasar Horst Seehofer ya yi barazanar fara mayar da bakin haure daga kan iyakar Jamus nan da makwanni biyu masu zuwa, in har ba a samar da wata mafita ba dangane da batun bakin hauren.
Shi dai Seehofer da ya kasance dan jam'iyyar CSU da ke zaman abokiyar takwaitakar jam'iyyar Merkel din CDU a tsahon shekaru, ya yi wannan barazana ce yayin wani taron manema labarai da jam'iyyar tasa ta gudanar, biyo bayan kwanakin da suka shafe suna musayar yawu tsakaninsa da shugabar gwamnatin kan batun 'yan gudun hijira da bakin haure.
A jawabinta shugabar gwamnati ta nunar da cewa jam'iyyun biyu na CDU da CSU suna da manufa guda domin inganta yanayin shigowar bakin haure kasar da kuma kokarin rage yawaitar kwararowar bakin hauren domin gudun ka da a maimaita abin da ya afku a shekara ta 2015, sai dai ta ce ba za ta iya zartas da hukunci ita kadai kai tsaye ba tana mai cewa:
"Bama son mu dauki mataki mu kadai. Kamar yadda na bayyana a baya, a nan gaba ba za mu kyale 'yan gudun hijira da aka riga aka yi musu rijista a wata kasa su shigo kasarmu ba, kamar yadda yarjejeniyar Dublin ta tanadar, mun kuma amince cewa a Jamus za mu yi aiki kan batun 'yan gudun hijira tare da makwabtanmu na Turai. Na tattauna batun hada hannu da Horst Seehofer dole shugabar gwamnati da ministan cikin gida su tattauna a tsakaninsu. Matsalar tsaro a Jamus ba abu ne mai sauki ba , a dangane da haka ya zamo shi ne abin da ke kan gaba da ya kamata mu bai wa muhimmanci."
Merkel ta kara da cewa za ta tattauna da takwarorinta na kungiyar EU yayin taron kungiyar da zai gudana a ranakun 28 da 29 ga wannan wata na Yuni da muke ciki. A nasa bangaren ministan cikin gidan Jamus din Horst Seehofer ya nunar da cewa zai so tasu ta zo daya shi da shugabar gwamnatin, inda ya ce:
"Idan muka cimma matsaya guda wato batun mayar da bakin haure daga kan iyaka a cikin watan nan na Yuni a matakin Turai ko kuma cikin yarjejjeniyar kasa da kasa, zamu yi farin ciki da hakan. Muna yi wa shugabar gwamnati fatan alkhairi akai. Sai dai har yanzu muna nan a kan bakanmu, na cewa in har ba a cimma matsaya ba kan wannan batu, tilas mu fara hana mutane shigowa kasarmu tun daga kan iyaka na take. Jam'iyyar CSU na goyon bayan duk wata mafita kan wannan batu daga nahiyar Turai."
Tuni dai Merkel ta sa kafa ta yi fatali da wannan barazanar ta ministan cikin gida Seehofer tana mai cewa babau wani mataki da za a dauka in har ba a samu mafita ta bai daya daga sauran kasashen Turai ba, tana mai gargadin sa da jam'iyyarsa ta CSU da cewa kada fa su manta ita ce ke da wuka da nama a wajen zartas da tsare-tsaren gwamnati.