1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon sojin Siriya ya sami daurin rai da rai

Abdullahi Tanko Bala
January 13, 2022

Wata kotu a Jamus ta yanke wa wani tsohon kanar na sojin Siriya Anwar Raslan hukuncin daurin rai da rai a gidan yari bayan samun sa da laifin azabtarwa da kuma kisan jama'a

https://p.dw.com/p/45UTT
Deutschland | Prozess um Staatsfolter in Syrien
Hoto: Thomas Frey/dpa/picture alliance

Kotun ta sami Anwar Raslan da kashe mutane 27 a gidan yarin Al-Khatib dake birnin Damascus.

An zartar da hukuncin ne karkashin dokokin kasa da kasa da suka da suka bada damar yi wa mutanen da ake tuhuma da laifukan yaki shari'a a wasu kasashe.

Wannan shine karon farko da kotun dake Koblenz a Jamus ta yanke irin wannan hukunci kan laifukan cin zarafin al'umma a Siriya.

Raslan mai shekaru 58 da haihuwa ya musanta azabtar da jama'a ko kuma bada umarnin azabtar da su.

An aikata laifukan ne a tsakanin shekarun 2011 da 2012 lokacin farkon yakin basasar Siriya.