1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wadanda da suka kamu da cutar coronavirus ya ragu a Jamus

Abdoulaye Mamane Amadou
April 6, 2020

Adadin sabbin kamun cutar coronavirus a Jamus ya karu da mutum 3,677 a cikin sa'a'o'i 24 wanda ya kawo yawan wadanda ke dauke da cutar ya zuwa mutum 95,391.

https://p.dw.com/p/3aUQA
Deutschland Dortmund Corona Behandlungszentum im Signal-Iduna-Park
Hoto: picture-alliance/dpa/Borussia Dortmund/BVB/A. Simoes

Wannan dai shine karo na hudu a jere da ake samun raguwar wadanda suka kamu da cutar a Jamus kamar yadda alkaluma da cibiyar yaki da cutattuka masu yaduwa ta Robert Koch suka nunar a wannan Litinin.

Tun daga  farko a ranar Lahadi Jami'ar Johns Hopkins ta Amirka ta ce kasar Jamus ta doshi adadin mutun dubu 100 da suka kamu da kwayar cutar Covid-19 a yanzu haka, a yayin da ta ke wallafa wani binciken da ta gudanar.

Rahoton ya ce adadin wadanda suka gamu da ajalinsu sakamakon cutar ta Coronavirus a kasar ta Jamus sun haura mutum 1,570

Jami'ar ta Johns Hopkins  na gudanar da nata binciken ne da ya sha bam-bam da na cibiyar Robert Koch Institut, ta kasar Jamus wacce tun daga farko ta ce za a iya samun adadi mafi karanci na wadanda suka kamu da cutar corona a yamacin lahadi.