Jamus za ta soma janye wasu dokoki takaita zirga-zirga
April 13, 2020Talla
Wata cibiyar bincike a kan sha'anin kiwon lafiya Robert-Koch-Institut ta ce fiye da rabin addadin mutane da suka kamu da cuta Coronavirus a Jamus sun warke, daga cikin mutane dubu 123 da suka kamu da cutar dubu 64 sun samu lafiya. Sannan a kwanaki na uku jere addadin masu mutuwa da masu kamuwa da cutar ya yi kasa kwarai.