Jamus na karancin kwararrun ma'aikata
June 5, 2023Talla
A wannan Litinin din ce dai ministocin na Jamus guda biyu Annalena Baerbock da Hubertus Heil suka fara wani rangadin aikin kwanaki uku, na zakulo ma'aikatan aikin jinya da kasar ke karanci a wannan kasa ta kudancin Amurka.
Baerbock ta ce tuni Jamus ta fara karbar ma'aikatan jinya da na bangaren aikin lantarki daga Brazil da Columbiya da hannu biyu, kuma suna muradin fadada wannan dangantakar.
A cewar Heil a daya hannun, a halin yanzu 'yan Brazil 200 ne ke aikin jinya a Jamus, sashin da ke fama da karancin kwararrun ma'aikata a cikin masana'antu da yawa.