Nijar: Jamus na son a yi sulhu
August 7, 2023Jamus ta shawarci kungiyar ECOWAS ko kuma CEDEAO da ta bi hanyoyin tattaunawa don warware rikicin juyin mulki a Nijar, bayan cikar wa'adin da ta ba wa sojoji na su dawo da hambararren shugaba kasar kan kujerarsa ko kuma a kowar da su da karfin tuwo.
A yayin da yake tsokaci kan wannan batu a birnin Berlin, mai magana da yawun ministar harkokin wajen Jamus ya nemi da a ci gaba da tattaunawa tsakanin majalisar sojojin da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika domin kauce wa matakin soji.
Sebastian Fischer ya kuma kara da cewa kungiyar ta ECOWAS ta ba da tabbacin cewa tana ci gaba da yin amfani da diflomasiya da kuma kakaba takunkumai kan tattalin arzikin Nijar don matsa lamba ga sojojin, kuma yanzu haka wadannan matakai sun fara yin tasiri ga kasar.
Baya ga Jamus, Italiya ma ta bukaci kungiyar kasashen Yammacin Afrikan da ta kauce wa daukar matakin soja a kan Nijar don gudun dagulewar lamura a cikin kasar da kuma yankin Sahel.
Sai dai a daya gefe kuma kasashen Mali da Burkina Faso da tun farko sun nuna goyoyn baya ga juyin mulkin, sun sanar da aike wata tawaga karkashin Abdoulaye Maïga domin jaddada goyon baya ga al'ummar Nijar a wannan lokaci mai matukar wahala.