1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yawan mutanen da suka mutu da Coranavirus a Jamus ya karu

Abdourahamane Hassane MNA
March 19, 2020

Wata cibiyar bincike a kan annoba da ake kira da sunan Robert Koch ta ce yawan mutane da ke dauke da kywayoyin cutar Coronavirus a Jamus ya haura sama da dubu goma.

https://p.dw.com/p/3ZiJ8
Deutschland Coronavirus Hamstern
Hoto: picture-alliance/dpa/R. Traut

A wani binciken da cibiyar ta bayana ta yawan ya karu da sama da mutum dubu da dari takwas a cikin sa'o'i 24 kawai. Kawo yanzu mutane guda 20 suka rasa rayukansu a sakamakon cutar a Jamus, yayin da alkalluman mutane da suka mutu da cutar ta Coronavirus  a duniya ya kai dubu tara.