Jamus ta kaddamar da kamfanin samar da magunguna a Rwanda
December 18, 2023Jamus ta ce kamfanin samar da magunguna na BioNtech da ta kaddamar a birnin Kigali na kasar Rwanda, wata alama ce ta kyakkyawar alaka da kuma hadin kai da ke tsakanin nahiyar Afirka da Turai.
karin bayani:Shari'ar kisan kiyashin Ruwanda a Paris
Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock, wadda ke ziyarar aiki yanzu haka a Rwanda, ta ce duniya ta gaza matuka wajen samar da magungunan rigakafi ga kowa da kowa a duk lokacin da wata annobar cuta ta barke, wannan dalili ne ya zaburar da Jamus wajen ganin da samar da mafita ga al'ummar Afirka da ma duniya.
Karin bayni:Rwanda ta fara rage cunkoson gidajen yari
Daga cikin magungunan da za a samar a kamfanin na birnin Kigali, sun hada da na rigakafin cutar Covid-19 da zazzabin cizon sauro wato maleriya da kuma na tarin fuka.