Jamus ta nemi afuwar 'yan Girka kan laifukan 'yan Nazi
October 31, 2024Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya nemi afuwar 'yan kasar Girka kan laifukan da gwamnatin 'yan Nazi ta aikata musu a lokacin yakin duniya na biyu, a yayin ziyarar da ya kai a wannan Alhamis a wani kauyen kasar Girkar da ake kira 'Cretan' inda yan Nazi suka aikata abin ya kira da 'abin kunya'.
A yayin wani jawabi mai sosa rai da ya gabatar a cikin harshen Latin a tsibirin Kandanos wanda 'yan Nazi suka shafe daga doron kasa a ranar uku ga watan Yuni na shekarar 1941, Mista Steinmeier ya ce 'A yau ina so in nemi gafararku da sunan Jamus'.
Frank-Walter Steinmeier shine shugaba kasar Jamus na farko da ke kai ziyara a wannan tsibiri da ke kudancin Girka, inda ya samu tarba daga al'ummar Kandanos suna daga alluna tare da rera wakoki na yin kira da a yi musu adalci a kan gaza cika alkawarin da Jamus ta dauka na biyansu diyya.