1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta nuna gazawa a harin kasuwar Berlin

Gazali Abdou Tasawa
December 20, 2017

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta amince cewa Jamus ta nuna gazawa wajen hana aukuwar harin ta'addancin da aka kai a kasuwar Kirsimeti ta birnin Berlin a bara da rashin kula da mutanen da harin ya ritsa da su. 

https://p.dw.com/p/2pgGt
Berlin Gedenken Breitscheidplatz Angela Merkel
Hoto: Reuters/F. Bensch

 Angela Merkel ta bayyana haka ne a jiya Talata albarkacin cikar shekara daya da kai harin kasuwar Kirsimetin birnin na Berlin wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12 a yayin da wasu kimanin dari suka ji rauni.

Da take bayani a gaban jama'a a wurin taron karrama kushewun mutanen da suka rasu a cikin harin, Merkel ta nuna alhininta da ma aniyar kawo gyara a nan gaba domin kauce wa sake aukuwar irin wannan hari nan gaba.

Shi ma dai daga nashi bangare shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya bayyana cewa lalle kasar ta nuna gazawa wajen hana aukuwar wannan hari da ma wajen kula da wadanda harin ya ritsa da su.

Yanzu haka dai kasuwannin Kirsimeti na ci gaba da ci a garuruwan kasar ta Jamus da dama a daidai lokacin da ake shirye-shiryen bukukuwan Kirsimetin na bana.