Jamus ta tsaurara matakan yaki da corona
August 27, 2020Talla
Angela Merkel dai na mai goyon bayan saka haraji na Euro 50, kwatankwacin Naira dubu 22, ga duk wanda aka kama ba ya sanye da takunkumin rufe baki da hanci a bainar jama'a. Har wayau tana mai bukatar saka dokar rage yawan taron mutane a cikin gida da ma waje.
Shugabar gwamnatin ta ce tana goyon bayan ministan lafiya da ya bukaci a daina gwajin cutar kyauta ga masu dawowa balaguro daga ketare.
A baya dai Jamus ta yi nasarar shawo kan annobar amma bisa janye dokokin da suka sanya a farkon shekarar nan ana yawan samun sabbin kamu da cutar a yanzu haka.