Martani kan cinikin makamai da Saudiyya
March 29, 2019Talla
Matakin na Jamus ya fuskanci kakkausar suka daga ciki da wajen kasar, inda kawancen kasashen Kungiyar Tarayyar Turai kamar Birtaniya da Faransa ke ganin matakin zai shafi ayyukan tsaro na hadin gwiwa.
Kungiyoyin kare hakkin fararen hula sun yi maraba da matsayar Jamus na daina fitar da manyan makaman yaki da sunan ciniki zuwa Saudiyya da ma sauran kasashen da ake zargi da hannu a yakin Yemen.