1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta yaye daliban kwallejin Islamiyya

Ahmed Salisu
June 15, 2021

Hukumomi a Jamus sun yaye zubin farko na daliban makarantar horon malaman addinin Islama sha'anin da ya danganci limanci da wa'azin Musulunci a kasar.

https://p.dw.com/p/3uxtk
Deutschland Islamkolleg Symbolbild
Hoto: Hans-Juergen Bauer/epd

Hikimar kafa irin wannan makaranta da ke birnin Osnabruck a Arewa maso yammacin Jamus ita ce ba da horo ga limamai da ma wadandan ke wa addinin Musulunci hidima a matakai daban-daban, kuma mahukuntan na Jamus sun ce sun yi hakan ne don kauce wa yaduwar malamai masu tsattsauran ra'ayi a kasar. 

Ender Cetin da ke cikin wadanda suka sami horon ya ce matakin ya dace. Mai shekaru 45 da haihuwa wanda asalinsa dan Turkiyya ne, Cetin ya ce horon ya kara masa fahimta kan lamuran addini da na zamantawa.

Bildergalerie Universität Tübingen
Hoto: imago/epd

Mata ma ba a barsu a baya ba wajen samun wannan horo da ya dangaci tafiyar da harkokin addinin na Islama kamar yadda Bülent Ucar farfesa a fannin nazarin addinin Islama a jami'ar Osnabrück ya shaidawa DW.

Kimanin kashi 20 cikin dari na wadanda suka samu horon mata ne kuma an gayyatosu daga bangarori daban-daban na musulmi mazauna Jamus cikinsu kuwa akwai 'yan Turkiyya da Bosniya da Larabawa da ma wadanda suka karbi addinin Islama daga baya.

Shi dai wannan horo wanda na shekaru biyu ne, shiri ne da za a ci gaba da yinsa kamar yadda hukumomi suka ambata kuma tuni ma jama'a da dama da ma masu rike da madafun iko suka fara maraba da shi. Horst Seehofer da ke rike da mukamin ministan cikin gida wanda ofishinsa ke kula da harkokin addininai na daga cikin wadana suka yi maraba da shirin, inda ya ce hakan zai kara daidaita lamura da ma tallafa wa mabiya addinin Islama a Jamus ta fuskoki da dama.

Deutschland Kiel | Imam
Hoto: Frank Molter/dpa/picture alliance

Haka ma abin yake ga kungiyar limaman addinin islama ta Jamus inda shugabanta Aiman Mazyek ya ce irin wannan horo zai share fagen kara ilimi ga limamai da sauran masu yi  wa addini hidima sannan zai taimaka wajen dora limaman kan tafarki da tsarin da masallatansu ke kai yayin a daya hannun Farfesa Bülent Ocar na Jami'ar Osnabrück ya yi fatan ganin limamai da dama sun amfana daga irin abin da suka koya don tafiyar da ayyukansu yadda ya dace.

Ina fatan limamanmu na Jamus su amfana da abubuwan da suka koya domin su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata da ma yanayin zamantawa da al'ummar kasa da wadanda suka fito daga tushe guda don samun fahimtar juna yadda ya kamata.

Wani abu har wa yau da Farfesa Ucar da ma wandada ke da ruwa da tsaki kan wannan shiri na horas da limamai da ma wadanda ke yi wa addinin Islama hidima shi ne fatan ganin wadanda suka samu horon sun nakalci Jamusanci don samun sukunin fahimtar juna tsakaninsu da al'umma ta yadda ba za a samu kuskure ko rashi fahimtar juna a sakonnin da suke isarwa ba.