Jamus: Yaki da cin-zarafin mata a duniya
November 25, 2024Diana B. na daga cikin matan da suka tsira daga irin wannan matsalar, inda ta samu wurin zama ita da yaranta a gidan da aka tanada saboda bai wa mata da kananan yara mafaka bayan mijinta ya yi ta yi mata barazanar kisa. Rahotanni sun bayyana cewa, duka nau'ikan cin-zarafin mata na karuwa a Jamus. Rahotannin daga Hukumar 'Yan Sanda da ke Lura da fannin Aikata Muggan Laifuka sun nunar da cewa, a shekara ta 2023 da ta gabata laifukan da suka shafi cin-zarafin mata sun karu. An tabbatar da kisan mata 360, ta hanyoyin da ke da alaka da cin-zarafi da kuma rabuwa.
Ministar cikin gida ta Jamus Nancy Faeser ta bayyana cewa, ku san kullum ana kashe mata a Jamus hakan duk bayan mintuna uku mata da 'yara mata na fuskantar cin-zarafi a cikin gidajensu. Ta jaddada cewa hakan na faruwa ne, saboda sun kasance mata. Hukumar 'Yan Sanda da ke Lura da fannin Aikata Muggan Laifuka ta ce, mata 155 ne
Tsofaffin samari ko mazajensu suka kashe a 2023. Za a iya tuhumar wadanda aka samu da cin-zarafin mata a cikin gida Jamus da kisan kai, sai dai mafi akasari an fi yanke musu hukunci a kan cin-zarafi a cikin gida. A watanni da suka gabata ministar harkokin iyali ta Jamus din Lisa Paus ta jaddada cewa, akwai bukatar daukar matakan tsaro a kan masu musgunawa mata ba wai 'yan ta'adda da ke sara-suka kadai ba.