1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta ta karbi 'yan gudun hijirar sansanin Moria

Binta Aliyu Zurmi
September 16, 2020

Jamus za ta dauki sama da dubu daya da dari biyar na 'yan gudun hijirar sansanin Moria da gobara ta raba su da matsugunansu kari a kan kananan yara dari da hamsin da ta bayyana tun da farko.

https://p.dw.com/p/3iXHA
Griechenland Flüchtlinge Lesbos
Hoto: Getty Images/AFP/L. Gouliamaki

Tun bayan da gobara ta kama a sansanin na Moria da ke tsibirin Lesbos a kasar Girka 'yan gudun hijirar ke tarwatse a titi, wanda firai ministan kasar ya bukaci kasashen EU da su kawo mishi dauki.

Yanzu haka dai Jamus na shirin tarbar iyalan da tuni suka sami shaidar takardun zama a kasar ta Girka.

Faransa ma ta sanar da karbar kananan yara 150. Tuni dai kasashen EU ke kokarin ganin sun kaiwa 'yan gudun hijirar dauki daga cikin halin tagayara da suke ciki.