Jamus za ta bai wa Brazil tallafi
January 31, 2023Talla
Yayin da yake wata ziyarar aiki a kasar Brazil, shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya yi alkawarin bai wa Brazil din tallafin dala 215 domin kare dajin Amazon. A ziyarar ta sa a yankin Kudancin Amirka domin karfafa alakar kasuwanci tsakanin Jamus da kasashe masu karfin tattalin arziki a yankin, shugaba Scholz ya ce, gwamnatin Berlin na son hanzarta yarjejeniyar kasuwanci mara shinge tsakanin tarayyar Turai da kasashen yankin Mercosur.
Kasashen Jamus da Norway sun kuma amince da bayar da tallafin Yuro miliyan 35 ga Brazil, wanda suka dakatar da bayarwa a lokacin mulkin tsohon shugaban kasar Jair Bolsonaro.
Scholz ya kuma ce gwamnatocin Berlin da Brasilia sun yi tarayya wajen yin tir da mamayar da Rasha ta kaddamar a Ukraine.