1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sauyin yanayi: Jamus ta zaburar

Gero Rueter USU/LMJ
April 29, 2020

A wani jawabin da ta yi yayin taron kare mahalli, shugabar gwamnatin jamus Angela Merkel ta bayyana cewa daga watan Yuli mai zuwa kasarta za ta ninka yunkurin da ta ke yi wajen kare mahalli.

https://p.dw.com/p/3bZX7
Petersberger Klimadialog
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel yayin tattaunawa kan sauyin yanayiHoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Yayin jawabin nata, shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta bukaci kungiyar Tarayyar Turai EU, ta dauki matakan rage shekarun da aka tsara domin tabbatar da rage amfani da sinadaran da ke gurbata mahalli daga shekara 2050 zuwa ta 2030. Duk da cewa a yanzu Jamus da sauran kasashen duniya sun mayar da hanakali ne wajen yaki da annobar Coroanvirus, Merkel din ta nuna jajircewarta a batun yaki da sauyin yananyi, inda ta bayyana cewa daga watan Yuli mai zuwa lokacin da Jamus din za ta karbi jagorancin karba-karba na kungiyar EU, kasar za ta fito da matakai da za su tsaurara yaki da gurbacewar mahalli.

Wa'adin shekaru 30 ya yi nisa

A cewar Angela Merkel cikin yarjejeniyar da kungiyar Tarayyar Turai ta yi, suna son cimma bukatar rage dumamar yanayin daga yanzu zuwa shekara ta 2050, amma a ganinta wa'adin shekaru 30 nan gaba ya yi nisa, a dangane da haka za ta yi maraba da sabon tsari mafi kusa da zai fara aiki nan take, tsarin da kungiyar EU ta yi wanda kafin nan da shekaru 10 za a iya rage kaso 50 zuwa kaso 55 cikin 100 na dumamar yananyin da duniya ke fuskanta.
Amma a cewar sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres duk irin wannan yunkuri da hobbasa da shugabanni irin na Jamus ke yi, ba zai cimma nasaraba muddin sauran kasashen da ke da manyan masana'antu ba su dauki yaki da dumamar yananyi da muhimmanci ba: "Ka da mu manta cewa kasashe 20  mafiya karfin tattalin arziki wato G20 ne suka fi fitar da hayaki da ke gurbata muhalli, kusan kaso 80 cikin 100. Haka zalika sune ke mallakar kaso 85 cikin 100 na tattalin arzikin duniya. Dole dukkansu su tattabar da kawar da hayaki mai gurbata muhalli nan da shekaru 30 masu zuwa."

Petersberger Klimadialog
Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio GuterresHoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Kasashe masu karfi su dauki mataki

Dama dai ko da yarjejeniyar kare muhalli ta duniya da aka cimma a birnin Paris na kasar Faransa, ta yi nasara ne sakamkon amincewa da ita da manyan kasashen duniya da ke da karfin masana'antu wato Amirka da Chaina suka yi, a dangane da haka masana ke cewa kafin duniya ta ga sauyi a bangaren hayaki mai gurbata muhalli, tilas wadannan kasashen su nuna da gaske suke yi, amma in ba haka ba duniya na cikin hadarin da gurbacewar muhalli zai haifar, abin da zai shafi rayuwar duka al'umma.