1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gangamin bukatar daukar mataki kan muhalli

Zainab Mohammed Abubakar
September 20, 2019

A daidai lokacin da dubban daruruwan mutane ke gangamin bukatar karin matakai na kare muhalli a sassa daban daban, gwamnatin Jamus za ta kashe Euro biliyan 54 kan matsalar sauyin yanayi.

https://p.dw.com/p/3PxV0
Karikatur Klimakabinett englisch

Bayan tattaunawar awoyi 18, gwamnatin hadakar ta Jamus ta sanar da cimma matakai masu yawa da suka kunshi kulawa ta musamman da za'a rika yi a duk a shekara, a wani mataki na cimma burin da aka sanya gaba dangane muhalli.

Mahukuntan na Jamus za su gabatar da tsarin matakan nasu da suka hada da shawo kan hayaki mai guba daga sashin makamashi da masana'antu da zuba jari a motocin da ke amfani da wutar lantarki da na sufuri.  

Dubban daruruwan dalibai da matasa nedai suka hade a yajin aiki da gangamin adawa da yadda gwamnatin ke yi wa matsalar sauyin yanayi rikon sakainar kashi.