Jamus za ta kori miyagun baki daga kasar
January 12, 2016Matakin da na a matsayin wani martani ga al'amarin cin zarafin daruruwan mata da wasu mazaje bakin haure suka aikata a jajibirin shiga sabuwar shekara ta 2016 a birnin Kolon.
Ministan shari'a na kasar Jamus Heiko Maas ya ce dole masu aikata miyagun laifuka a Jamus su fiskanci hukunci. Kuma kora daga cikin kasar na daga cikin hukuncin da dokar ta tanada ga baki 'yan asalin kasashen waje da za a samu da aikata laifi. Dan haka ne suka saukaka hanyar daukar matakin iya korar duk wani dan asalin kasar waje da zai aikata lafin cin zarafin wani mutun ko wani jami'in tsaro.
A karkashin sabuwar dokar, daga yanzu dai duk wani dan asalin kasashen waje mazaunin kasar Jamus da kotu za ta yankewa hukunci ko da na talala ne kan aikata wani laifi to kuwa za a kore shi daga cikin kasar baki daya.