Jamus na bincike kan maganin Coronavirus
March 16, 2020Talla
Heiko Maas ya fadi haka ne bayan da shugaban Amirka Donald Trump ya nuna sha'awar sayen hakkin mallakar maganin da wani kamfanin Jamus ya hada.
Maas ya ce wani kwararren a fannin bincike na kasar Jamus ya taka rawa sosai wurin gudanar da bincike domin samar da maganin cutar, a don haka kasar ba za ta bari wani ya mallaki sakamakon ba.
Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da Amirka ke shirin fara gwajin wani samfurin maganin cutar kan wasu matasa 45.