Jamus: Zaben 'yan majalisa a jihar Saarland
March 26, 2017Talla
Sai dai wannan zabe ana kallonsa a matsayin zakaran gwajin dafi musamman ga Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel, yayin da watanni shida suka rage ga babban zaben kasar, inda jam'iyyarta ta CDU ke fuskantar barazana daga abokiyar kawancenta ta SPD tun bayan da tsohon shugaban majalisar Tarayar Turai Martin Schulz ya sanar da aniyarsa ta neman shugabancin gwamnatin ta Jamus.
Sai dai a wannan yanki da jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ke da karfi, binciken jin ra'ayin jama'a ya nunar cewa kashi 35 zuwa 37 cikin 100 na masu zaben na goyon bayan wannan jam'iyya, yayin da binciken ya nunar cewa jam'iyyar SPD za ta iya samun kashi 32 zuwa 34 cikin 100 na masu zaben.