Nijar: Dakarun Faransa sun fice
July 10, 2019Dakarun Faransan 600 ne dai suka kafa sansaninsu a Madama cikin jihar Agadez da ke kan iyakar Jamhuriyar ta Nijar da makwabciyarta Libiya, tun cikin watan Oktoba na shekara ta 2014. Rahotanni sun nunar da cewa dakarun za su ketara ne zuwa kasashen Mali da Burkina Faso da Chadi da ke fama da matsanancin hare-haren 'yan ta'adda masu kaifin kishin addini a 'yan kwanakin baya-bayan nan. A jawabinsa ministan tsaro na Jamhuriyar ta Nijar Kalla Muntari ya ce Faransan na da 'yancin janye dakarunta daga kasar a duk lokacin da ta so, kuma gwamnati na da masaniya kan matakin kana dakarun gwamnati da ke Madama din za su yi iya kokarinsu domin kare kasar daga ko wacce irin barazanar tsaro.
Dama dai kungiyoyin farar hula da wasu daga al'ummar kasar sun jima suna adawa da kasancewar sojojin kasashen ketare ciki kuwa har da Faransan a Jamhuriyar ta Nijar. Musa Changari na daga cikin masu fafutukar da ke adawa da kasancewar sojojin kasashen wajen a kasarsa, a ta bakinsa yana maraba da ficewar sojojin Faransan kuma suna ma fatan sun tafi ke nan baki daya. Masu fashin baki kuwa na ganin cewa Faransan na tsoron kada wani abu ya sami sojojinta sakamakon rikicin da ake fama da shi a Libiya, kuma akwai rade-radin sojojin kasashen Larabawa ka iya zuwa domin kafa nasu sansanin a wannan yanki.