SiyasaAsiya
Gobara a Japan ta hallaka mutane da dama
December 17, 2021Talla
Kimanin mutane 27 ne ake fargabar sun mutu a sanadiyyar wata gobara da ta tashi a wani gidan haya mai bene takwas a birnin Osaka na kasar Japan.
'Yan sandan kasar sun ce sun kaddamar da bincike don gano musabbabin tashin gobarar. Kafar yada labaran Japan ta NHK ta nuna yadda hayaki ke fitowa daga tagogin benen da lamarin ya faru.
Bayan mutane 27 da suka hadu da ajalinsu hukumomi sun ce akwai mutum guda da ya tsira da rayuwarsa duk da munanan raunukan da ya samu.