Ministan kula da al'amuran shari'a na Japan ya ajiye mukamin
October 31, 2019Talla
Minista Katsuyuki Kawai ya bayyana wa manema labarai cewar ya ajiye mukamin ne bayan da jaridu suka ba da labarin cewa matarsa 'yar majalisa karya dokar zabe, sakamakon yadda ta biya masu yi ma ta farfaganda kudaden da suka wuce kima. Wannan shi ne karo na biyu ke nan da wani ministan ke yin marabus a cikin mako guda a Japan. A makon jiya ma minista kamfanonin da masana'antu ya yi marabus wanda shi ma kafofin yadda labarai suka zargeshi da bai wa masu zabe kudade kyauta.