Japan: Shekaru 72 da harin Amirka a Hiroshima
August 6, 2017A ranar 06 ga watan Agusta na shekarar 1945 da misalin karfe 08 da mintuna 15 agogon kasar ta Japan wani jirgin yakin kasar Amirka ya sako bam din na farko, sannan bayan kwanaki uku Amirkar ta sake sako wani bam na biyu na nukiliya a birnin Nagasaki wanda hakan ya sa Japan ta bada kai bori ya hau a ranar 15 ga watan na Augusta kwanaki shida baya, wanda ya kawo karshen yakin duniya na biyu.
Firaminista Shinzo Abe na Japan da ke magana a dandalin zaman lafiya na Hiroshima, ya ce kasar Japan za ta ci gaba da kokowa ta yaki da kaurace wa makaman nukiliya a duniya.
"Daga nan Hiroshima ina mai jaddada kira ga kasashen da ke da makaman nukiliya, da kuma wadanda ba su da shi, fatanmu shi ne na hada kan bangarorin biyu don samun duniya wadda babu makaman nukiliya a cikinta."
Bam din dai na farko ya haddasa mutuwar mutane dubu 140 a Hiroshima yayin da na biyun ya hallaka mutane dubu 74 birnin Nagasaki