Tuni da hari da makamin kare dangi na Hiroshima
August 6, 2020A yau shida ga watan Augusta ake cika shekaru sabain da biyar (75) da faruwar harin Hiroshima da Nagasaki na kasar Japan, Amirka ta soma jefa makamin Nukiliya na kare dangi a birnin Hiroshima kafin ta jefa na biyun a Nagasaki, lamarin da ya sa Japan mika wuya a yayin yakin duniya na biyu.
Al'umomin a kasar kan hadu a duk rana irinta ta yau don nuna alhini kan iftala'in da yayi sanadiyar rayukan Japanawa kimanin dubu dari da arba'in, amma a bana, annobar Corona ta rage ma taron da ke hada kan 'yan kasa dama baki daga kasashen duniya armashi.
Firaiminista Shinzo Abe a yayin jawabinsa, ya ce, kasar za ta yi duk mai yiyuwa wajen ganin an haramta amfani da duk wani na'ui na makamin nokiliya. Tarihi ya nuna cewa, hare-haren na Hiroshima da Nagasaki sun kasance karon farko da ake kai hari da makami mai guba kan bil'adama a duniya.