Japan ta bukaci matsin tattalin arziki a kan Koriya ta arewa
July 17, 2006Japan na nazarin ɗaukar wasu matakan matsin tattalin arziki a kan ƙasar Koriya ta arewa bayan watsi da Pyongyang ta yi da ƙudirin kwamitin sulhu na majalisar ɗinkin duniya wanda ya bukaci ta jingine shirin ta na makamai masu linzami. Ɗaukacin yan kwamitin sulhun na majalisar ɗinkin duniya sun kaɗa ƙuriár yin Allah wadai da gwajin makamai masu linzami da Koriya ta arewa ta yi tare kuma da buƙatar ta dakatar da dukkan wani shiri na makaman masu linzami, to amma Koriya ta arewan ta yi burus da wannan ƙudiri inda ta lashi takobin faɗaɗa makaman ta domin kariyar kan ta. Sakataren majalisar gudanarwa na ƙasar Japan Shinzo Abe ya gabatar da sabuwar shawara ta dakatar da baiwa koriya ta arewan kudade, da dakatar da huldodin cinikayya ta ita da kuma rike kadarorin ta dake Japan. ƙasar ta Koriya ta arewa ta dogara ne ga tallafin da take samu daga yan ƙasar Mazauna Japan. ƙudirin majalisar dinkin duniyar dai ya buƙaci ɗaukacin mambobin ƙasashe su dakatar da saye ko musayar kayayyakin fasahar zamani daga Koriya ta arewa da kuma dukkan wata hada hada ta kuɗaɗe. Bisa wannan kudiri Japan zata buƙaci sauran ƙasashe su haɗa hannu wajen aiwatar da matsin tattalin arziki a kan Koriya ta arewa.