1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Japan ta damu da halin dar-dar a tekun kudancin China

Mohammad Nasiru AwalFebruary 17, 2016

Gamaiyar kasa da kasa ba ta ji dadin matakan da Sin ke dauka a yankin tekun kudancin China ba, inda ta jibge makamai masu linzami.

https://p.dw.com/p/1Hwn1
China Raktenabwehrsystem HQ-9 Militärparade in Peking
Hoto: picture-alliance/dpa/Imaginechina/Ge Jinfh

Babban sakataren majalisar dokokin kasar Japan Yoshihide Suga ya nuna matukar damuwar kasarsa a kan rahotannin da ke cewa kasar Sin wato China ta girke makamai masu linzami da ke cin dogon zango a tekun kudancin Chinar. Yoshihide Suga ya fada wa wani taron amnema labarai a birnin Tokyo cewa kasarsa ba za ta yarda wannan mataki ba.

"Gamaiyar kasa da kasa ma ta damu da yunkurin Chinar na sauya halin da ake ciki tare da janyo zaman dar-dar a yankin sakamakon mamaya da kuma kwace wasu manyan filaye inda ta gina sansaninta a yankin kuma tana amfani da shi wajen ayyukan soji. Mun damu matuka da wannan matakin kuma Japan ba za ta amince da shi ba."

A wannan Larabar jami'an Taiwan da na Amirka sun fada wa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa China ta girke makamai masu linzami a tsibirin Woody. China dai ta ce kamata ya yi kafafan yada labaru na yamma sun mayar da hankali kan kokarinta na samar da tsaro ga sufurin jiragen ruwa a yankin.