Japan ta yi gargadi ga Koriya ta Arewa
September 6, 2016Kasar Japan din dai ta bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya tura cikakken sako zuwa Koriya ta Arewa tare da yin alawadai ga aikin harba makamai masu linzami har guda uku da kasar ta yi a ranar Litinin din da ta gabata. Jakadan kasar Japan a Majalisar Dinkin Duniyar Koro Bessho ne ya bayyana haka a wannan Talatar bayan wata tattaunawar sirri da Amirka ta kira domin mayar da martani bisa gwajin makaman na Koriya ta Arewa.
Shima da yake bayyana takacinsa dangane da gwajin makami masu linzamin da Koriya ta Arewan ta yi, jakadan kasar China a Majalisar Dinkin Duniya China Liu Jieyi cewa ya yi abin bakin ciki ne, ganin kasar ta Koriya ta Arewa ta aikata haka a lokacin da China ta karbi bakuncin shugabanni da suka halarci taron kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya na G20.