Japan ta ɗauki matakin takunkumi a kan ƙasar Burma
October 16, 2007A sakamakon tashe tashen hankulan da ke wakana a ƙasar Burma , Japon ta yanke shawara dakatar da wani sashe na tafllafin da ta ke baiwa wannan ƙasa.
HukumominTokyo, sun ɗauki wannan mataki, a matsayin takunkumi ga Myanmar, ta la´akari da mummunan matakin da sojojin ƙasar su ka ɗauka ga masu zanga-zanga a watan da ya gabata.
Komitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia,a makon da ya wuce, ya hiddo sanarwa, inda yayi Allah wadai ga azabar da gwamnatin Burma, ta ganawa masu zanga-zangar.
Ita ma Amurika, ta jaddada kira ga ƙasashen dunia, su maiyar da gwamnatin mulkin sojan Myanamar saniyar ware.
Saidai duk da tofin Allah tsine da su ke ci gaba da samu daga ƙasashen dunia, sojojin sun ce babu gudu babu ja da baya.
A nasa gefe, wakilin musamman na Majalisar Ɗinkin Dunia, Ibrahim Gambari na ci gaba da kai gwaro da mari, a yankin Asia , da zumar samar da hanyoyin kawo ƙarshen rikicin siyasa a ƙasar Burma.