Japan za ta rufe tashoshin nukliyar ta
May 5, 2012Shirin wanda aka fara ƙaddamar da shi a sama da shekara daya bayan hatsarin Fukushima ;ya hada kusan tashohi guda 50 da aka riga aka garke. Kuma tashar nukliya ta ƙarshe da ke yin aiki ta Tomari da ke a arewacin ƙasar har an fara aikin tsayar da i'ta.
Sama da mutane dubu biyar suka gudanar da wata marchi ta nuna murna ta yin bankwana da tashohin nukliyar; wanda hatsari da aka yi na tashar fukushima a cikin watan Maris na shekara bara a sakamakon igiya ruwa na tsunami da aka samu ya hadasa mutuwar duban rayukan jama'a.To sai wasu na ganin cewa wannan sabon al amari zai haifar da tsada da kuma ƙarancin wutar lantarki wada kusan kashi 50 cikin ɗari na lantarkin da ake sha a japan na zuwa ne daga tashoshin nukliyar.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Halima Balaraba Abbas