1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Japan za ta ƙaddamar da ayyukan gina ƙasa

March 18, 2011

Gwamnatin ƙasar Japan ta ce nan ba da daɗewa ba za ta fara gudanar da muhimman ayyukan sake gina ƙasar.

https://p.dw.com/p/10c7x
Naoto Kan shugaban gwamnatin JapanHoto: AP

Hukumomin a ƙasar Japan sun bada sanarwar cewa girgizar ƙasar da aka yi a ranar sha ɗaya ga wannan wata a yankin arewa maso gabashin ƙasar ta kasance mafi muni da aka taɓa yi tun bayan wadda aka yi a yankin Kobe na ƙasar a shekara ta 1995. Mutane dai kusan 6539 suka mutu a cikin girgizar wacce ta haddasa igiyar ruwa yayin da wasu sama da dubu goma suka yi ɓatan dabo. Shugaban gwamnatin ƙasar Naoto Kan ya ce nan bada jumawa ba za su shiga aikin sake gina ƙasar.

Haka zalika ma'aikata na cigaba da ƙoƙari a cibiyoyin nukiliyar na uku dana huɗu inda suke amfani da ruwa wajen sanyaya murhunan. Gwamnatocin ƙasashen ƙetare na ta baiwa jama'ar su shawara su fice daga birnin Tokyo su kuma ƙaurace wa yankin arewa maso gabashin ƙasar. Ofisoshin jakadanci da dama waɗanda suka haɗa da na Jamus sun koma birnin Osaka dake kudancin Japan zuwa wani lokaci na wucin gadi.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita: Mohammad Nasiru Awal