Jaridun Jamus: Dubun dubatan ma'aikatan bogi a Najeriya
March 4, 2016Za mu fara sharhin jaridun Jamus kan nahiyarmu ta Afirka da jaridar Süddeutsche Zeitung da a wannan mako ta leka tarayyar Najeriya tana mai cewa "kaddamar da yaki da ma'aikatan bogi don tsabtace hukumomin gwamnati.
Ta ce a kwanan nan ne gwamnatin Najeriya ta soke sunayen dubun dubatan ma'aikatan gwamnati daga jerin masu karban albashi a kasar. Jaridar ta ce da farko za a dauka wannan mataki mai tsauri, amma idan aka yi masa karatun ta natsu za a ga cewa da kwakkwarar hujja, domin wadannan ma'aikata ne na bogi wadanda dubunsu ta cika sakamakon cikakken bincike da ma'aikatar kudi ta kasar ta yi. Tsabtace ma'aikatun gwamnatin wani karin mataki ne a yaki da cin hanci da rashawa da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati.
Wasan boya tsakanin 'yan sanda da 'yan adawa
Daga Najeriya sai kasar Yuganda inda jaridar Die Tageszeitung ta labarto mana yadda 'yan sanda a Yuganda ke muzuguna wa 'yan adawa da 'yan jarida tun lokacin zaben da aka gudanar a kasar.
Ta ce a wani lungun da ke kusa da fadar shugaban kasa 'yan sanda sun yi ta farautar wani alade da aka yi masa fenti ruwan dorawa da 'yan adawa suka saki. Ruwan dorawa dai shi ne launin jam'iyyar shugaba Yoweri Museveni wanda ya sake lashe zaben kasar. Tun bayan wannan zaben ne kuma ake wasan boya tsakanin 'yan adawa da 'yan sanda a Kampala babban birnin kasar. Su kuma 'yan jarida ana yi musu feshin barkono da zarar sun je kusa da wuraren da ake fito na fito da 'yan adawa. Yayin da shi kuma madugun 'yan adawa Kizza Besigye da ya sha kaye a zaben, kusan yanzu haka ana yi masa daurin talala ne a gidansa.
Barclays Bank na Birtaniya zai yi bankwana da Afirka
Bankin Barclays na Birtaniya ya fara janyewa daga nahiyar Afirka inji jaridar Franfurter Allgemeine Zeitung, inda ta kara da cewa bankin na neman masu sayen kadarorinsa.
Ta ce shekaru kalilan da suka gabata tsohon shugaban Barclays Bank Bob Diamond ya kwatanta Afirka a matsayin nahiya mai samun gagarumar bunkasar tattalin arziki. Amma sabon shugaban bankin na Birtaniya ya yi juyin waina. Bayan tsawon watanni ana jita-jita a ranar Talata da ta gabata Barclays Bank ya ba da sanarwar yin bankwana da Afirka sannan nan da shekaru biyu zuwa uku zai sayar wa Barclays Africa Group kasonsa.
Tserereniyar sayen filayen noma a Afirka
Har yanzu dai muna kan batun na gwamna masu gida rana, inda jaridar Süddeutsche Zeitung ta rawaito cewa masu zuba jari na kasa da kasa na rige-rigen sayen karin filayen noma a kasashe masu tasowa. Talakawa kuwa sai kallo, lamarin da ke barazanar haddasa rikice-rikice. Wani kiyasin kungiyar agaji ta Oxfam na cewa daga shekarar 2001, filayen noma kimanin eka miliyan 230 aka sayar a kasashe masu tasowa, musamman ma a nahiyar Afirka. Jaridar ta ce dalilai sun bambamta na sayen filayen. Yayin da a wasu yankunan ana zuba jari don inganta noman kayan abinci, a wasu wuraren kuwa harkar kasuwanci masu zuba jarin suka sa a gaba.