1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya da Mali sun dau hankalin Jaridun Jamus

Suleiman Babayo LMJ
August 9, 2024

Zanga-zangar Najeriya da kisan sojojin hayar Rasha a Mali da ya haddasa gurguncewar alaka tsakanin Mali da Ukraine, na cikin batutuwan da jaridun Jamus suka mayar da hankali a kai.

https://p.dw.com/p/4jJ3m
Rasha | Sergei Lavrov | Alaka | Mali | Abdoulaye Diop | Tsami | Dangantaka | Ukraine
Ministan harkokin wajen Mali Abdoulaye Diop da takwaransa na Rasha Sergei LavrovHoto: Alexander Shcherbak/TASS/dpa/picture alliance

Za mu fara da jaridar Weltplus da ta mayar da hankali kan yadda aka halaka sojojin haya na kamfanin Wagner na Rasha a kasar Mali da ke yankin yammacin Afirka, abin da ya janyo kasar ta Mali yanke hulda da Ukraine kan wasu kalamai da ake dangantawa da hannun Kyiv din kan harin na Mali. Gwamnatin mulkin sojan Mali ta katse hulda nan take da Ukraine a wata sanarwa, saboda harin da aka kai kasar da ke zaman mafi girma tun bayan janyewar dakarun kasashen duniya daga Mali. Hakan na zuwa lokacin da ministan harkokin wajen Ukraine, Dmytro Kuleba ya kai ziyara zuwa kasashen Malawi da Zambiya da kuma Mauritius wadanda suka kada kuri'a  a kan kudirin Majalisar Dinkin Duniya na nuna kyama da kaddamar da yaki da Rasha ta yi a Ukraine din.

Tunusiya | Shugaban Kasa | Kais Saied | Firaminista | Sabo
Shugaba Kais Saied na TunusiyaHoto: Chokri Mahjoub/ZUMA Wire/IMAGO

Ita kuwa jaridar Zeit Online ta bayyana cewa Shugaba Kais Saied na Tunisiya wanda ya sallami Firaminista Ahmed Hachani daga bakin aiki  lokacin da ake fuskantar karancin ruwan sha da katsewar hasken wutar lantarki, ya nada Kamel Maddouri ministan kula da walwalar rayuwa a matsayin sabon firaministan kasar da ke yankin arewacin Afirka. Yayin da ake danganta matsalar da fari da aka fuskanta a kasar, sai dai Shugaba Saied yana ganin zagon kasa wasu suke masa gabanin zaben shugaban kasa da za a gudanar ranar shida ga watan Oktobar wannan shekara. A shekara ta 2019 shugaban ya hau mulki, kuma yana ci gaba da fadada karfinsa, wajen rusa majalisar dokoki da kame jiga-jigan 'yan adawa. 

Sudan | Yaki | Darfur | Yunwa
Matsalar yunwa a sansanin 'yan gudun hijra a SudanHoto: ERRFC

Sai kuma jaridar die Tageszeitung wadda ta ce ma'aikatan jinkai sun tabbatar da cewa ana fama da matsancinyar yunwa a sansanin 'yan gudun hijira na Dafur da ake kira Zamzam, sakamakon rikicin da ke faruwa a kasar Sudan. Edem Wosornu jami'ar diflomasiyar Majalisar Dinkin Duniya daga kasar Ghana da ke jogorancin hukumar jinkai ta majalisar, ta shaida wa Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa lokaci na kurewa game da taimakon mutanen sakamakon makara da aka yi, kana yaki na ci gaba da faruwa a kasar ta Sudan da kara haifar da 'yan gudun hijira. Yanzu haka akwai kimanin 'yan gudun hijira tsakanin dubu 500 zuwa dubu 800 da suka tsere, sakamakon rikici daga yankin El Fasher sakamakon fada da ake fafatawa tsakanin sojojin gwamnatin kasar ta Sudan da rundunar RSF, tun a watan Afrilun shekarar da ta gabata ta 2023.

Najeriya | Bola Ahmed Tinubu | Zanga-Zanga | Tsadar Rayuwa | Talakawa
Rikidewar zanga-zanga zuwa tarzoma a NajeriyaHoto: Kola Sulaimon/AFP

Har ila yau jaridar ta die Tageszeitung ta duba irin zanga-zangar da ake yi kan tsadar rayuwa a Najeriya, inda masu zanga-zangar suka yi watsi da bukatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta tattaunawa tare da cewa za su ci gaba da mamaye tituna na lokacin da suka tsara gudanar da wannan zanga-zanga a kasar mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka. Jaridar ta kara da cewa mutane da dama suka halaka, sakamakon wannan zanga-zangar. Shugaba Tinubu mai shekaru 72 a duniya ya yi jawabi ga 'yan Najeriya tare da neman hadin kai, domin magance yanayin da kasar ta samu kanta a ciki na tashin farashin kayayyaki. Shugaban ya kare matakan da gwamnatinsa take dauka na samar da ci-gaba tun lokacin da ya dauki madafun ikon kasar, bayan zaben da ya samu nasara a shekarar da ta gabata ta 2023.