Jaridun Jamus: Rashin tabbas a Kwango da Gambiya
December 23, 2016Bari mu fara da jaridar Süddeutsche Zeitung wadda ta ce a 'yan makonnin da suka gabata an samu labarai masu dadin ji daga nahiyar Afirka. Ta ce na farko shi ne a Ghana an zabi sabon shugaban kasa, wanda kuma ya fadi a zaben ya amince da zabin al'ummar kasa ba tare da an zubar da jini ba. Sai dai kuma duk wannan ci gaban, nahiyar ta Afirka na da tarin matsaloli wajen samun sauyin mulki cikin ruwan sanyi kuma ta tsarin demokradiyyya. Misali na baya-bayan nan shi ne a kasar Kwango inda duk da kawo karshen wa'adin mulkin Shugaba Joseph Kabila kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, amma maimakon shugaban ya shirya sabon zabe, sai kawai ya tura jami'an tsaro suka yi ta harbin masu zanga-zanga. A Gambiya ma dai Shugaba Yahya Jammeh ya yi amai lashe, bayan da a farko ya amince da shan kaye a zabe, daga baya ya yi fatali da sakamakon zaben.
Mayar da Jammeh saniyar ware
Ita ma jaridar Berliner Zeitung tsokaci ta yi kan rikicin siyasar kasar Gambiya tana mai cewa kungiyar habaka tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ta kuduri aniyar dora mai kalubalantar Jammeh kan mulki.
Ta ce bisa ga dukkan alamu kasashen duniya sun kama hanyar mayar da Shugaba Yahya Jammeh na Gambiya saniyar ware bisa matakin da ya dauka na kin amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa da ya sha kaye bayan da farko ya yi na'am da sakamakon har ma ya taya jagoran 'yan adawa Adama Barrow murnar lashe zaben. Jaridar ta ce a wani taron koli na musamman da suka yi a birnin Abujan Najeriya, shugabannin ECOWAS sun nuna amincewarsu ga Adama Barrow a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar daya ga watan Disamba. Sun kuma sha alwashin daukar dukkan matakan da suka dace na aiwatar da zabin al'umma da zai kai ga rantsar da Barrow a ranar 19 ga watan Janairu. Daga cikin matakan akwai yiwuwar tura dakaru. A daidai lokacin da kungiyoyin farar hula a Gambiya ke kara daga murya suna kira ga Shugaba Jammeh wanda shafe shekaru 22 kan karagar mulki da ya rungumi kaddara.
Bunkasar tattali arziki na barazanar zama alakakai
Kasar Habasha na jin jiki sakamakon ci gabar da kasar ke samu, inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung.
Ta ce kasar Habasha wadda ta kasance abin koyi saboda bunkasar tattalin arziki mai yawa, yanzu tana fama da koma bayan tattalin arziki a daidai lokacin da al'ummar kasar ke kara nuna takaicinsu a dangane da manufofi masu tsauri kan mallakar filaye da gonaki da gwamnatin kama karya ke amfani da su. Kasar dai na da manyan gonakin gahawa da masara da dankalin turawa da dai sauran albarkatun gona. Baya ga haka akwai gonakin furanni da take sayar wa kasar Holland. Amma rashin kyaun yanayi musamman na El Nino da matakan ba sani ba sabo da mahukuntan birnin Addis Ababa ke dauka kan wani sashe na al'umma, sun sa kasar na fuskantar tawayar tattalin arziki.