1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kasashen Tarayyar Sahel cikin jaridun Jamus

Mouhamadou Awal Balarabe LMJ
July 12, 2024

Batun kafa kasashen Tarayyar Sahel da hannun Ruwanda a rikicin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, na daga cikin abubuwan da suka dauki hankulan jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/4iEi9
Mali | Assimi Goita | Nijar | Janar Abdourahamane Tiani | Burkina Faso | Kyaftin Ibrahim Traore | AES
Assimi Goita na Mali da Janar Abdourahamane Tiani na Nijar da Kyaftin Ibrahim Traore na Burkina Faso Hoto: Mahamadou Hamidou/REUTERS

Welt online ta mayar da hankali ne kan sharar fage da shugabannin mulkin soja na Mali da Burkina Faso da Nijar suka yi, na kafa Tarayyar Kasashen Sahel. Jaridar ta ce abubuwa da yawa sun faru tun bayan juyin mulkin da suka gudana a wadannan kasashen a tsakanin 2020 zuwa 2023, lamarin da ya kai jami'an sojan Mali da Burkina Faso da Nijar katse hulda da kasashen Yamma tare da rungumar Rasha. Jaridar ta kara da cewa gwamnatocin mulkin sojan na zargin kungiyar ECOWAS ko CEDEAO da zama 'yar amshin kasar Faransa da ta yi musu mulkin mallaka, inda ta kakaba musu takunkuman da suka saba da dokokin kasa da kasa maimakon taimaka musu yakar ta'addanci da ke ci musu tuwo a kwarya. Sai dai jaridar ta ce watanni shida kafin takardar raba garin ta fara aiki, har yanzu kasashen yammacin Afirka ba su cire tsammanin dawowar Mali da Burkina Faso da Jamhuriyar ta Nijar cikin dangi ba.

Jamhuriyar Dimukuradiyya Kwangon | Goma | Rikici | Gudun Hijira
Rikicin Jamhuriyar Dimukuradiyya Kwangon dai, ya tilasta dubban mutane yin hijiraHoto: Moses Sawasawa/AP Photo/picture alliance

Ita kuwa a nata sharhin, die tageszeitung ta ce Majalisar Dinkin Duniya ta gano cewar Ruwanda na da hannu dumu-dumu a rikicin gabashin Kwango, inda take goyon bayan 'yan tawayen M23. Jaridar ta ce tallafin dabarun yaki da fadar mulki ta Kigali ke bai wa dubban dakaru da ke kalubalantar sojojin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, na sa 'yan tawayen na M23 samun nasara a gabashin Kwangon. Ta ce sojojin Rawanda na taka muhimmiyar rawa kai tsaye ko a fakaice, a nasarorin baya-bayan nan da kungiyar 'yan tawayen ta M23 ke samu a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.  Jaridar ta ce ba kasafai Majalisar Dinkin Duniya ke wallafa rahoto kan zargin Ruwanda da hannu a rikicin Kwangon ba, amma masu bincike sun kiyasta cewar adadin sojojin Ruwanda a sansanin M23 a lardin Kivu ya kai  3,000 zuwa 4,000, baya ga makamai na zamani da take samar musu.

Kamaru | Shugaban Kasa | Paul Biya | Brenda Biya
Shugaban kasar Kamaru Paul BiyaHoto: Daniel Beloumou Olomo/AFP/Getty Images

A daya bangaren kuwa, die tageszeitung ta yi tsokaci kan bayyana kanta, a matsayin 'yar madigo da 'yar shugaban kasar Kamaru Brenda Paul Biya ta yi a kafofin sada zumunta. Jaridar ta dasa ayar tambaya tana mai cewa, wai shin wannan mataki ne na gaban kanta da ke nuna cewa karanta ya kai tsaiko? Ko kuma hannunka mai sanda ne na musamman ga rikicin da makusantan Paul Biya ke yi, domin su gaje shi idan ta Allah ta kasance? Wai shin me ya sa dabi'ar neman jinsi da 'yar shugaban kasar Kamaru ta bayyana, ke zama abu mai daukar hankali? A amsar da ta bayar, die tageszeitung ta ce luwadi da madigo ba wai kawai abu ne da ake kyama ba, amma ana hukunta duk wanda aka samu da neman jinsi kamar yadda ake yi a yawancin kasashen Afirka. Amma a Kamaru, zargi ko yarfen aikata luwadi na iya shafawa mutum kashin kaji ko raba shi da mukaminsa kwata-kwata. Hukumomin kasar ma sun nunar da cewar an rabu da luwadi da madigo kwata-kwata a hukumance tun shekarar 2013, lamarin da ke tilasta wa masu neman jinsi na wannan kasa gudun hijira domin guje wa tsangwama da azabtarwa.