1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasa na neman kassara Senegal

Usman Shehu Usman ZUD
July 1, 2022

Rikicin siyasar kasar Senegal da halin yunwa a Gabashin Afirka gami da kokarin mayar wa Najeriya da kayan tarihin da aka sace mata lokacin mulkin mallaka na cikin abubuwan da suka dauki hankulan jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/4DWfe

Kasar Senegal na kara fadawa cikin rashin zaman lafiya. Bayan da aka yi watsi da jerin sunayen 'yan adawa na zaben 'yan majalisar dokoki, an yi tashe-tashen hankula da kashe-kashe. Zaben 'yan majalisar dokokin kasar da za a yi a ranar 31 ga watan Yuli a kasar Senegal, ya kasance gabanin zanga-zanga mai tsanani. Tuni dai mutane uku suka mutu a arangamar da aka yi a lokacin yakin neman zabe. A Senegal dai, Macky Sall bai fito fili ya sanar da ko zai tsaya takara a zaben shugaban kasa karo na uku a shekara ta 2024 ba - sabanin sashe na 27 na kundin tsarin mulkin kasar, wanda ya ba da damar wa'adi biyu a jere. 

Shugaban Senegal Macky Sall
Shugaban Senegal Macky SallHoto: John Thys/AFP

Ita kuma jaridar Berliner Zeitung ta ce nan ba da dadewa ba, dukkan tagulla na Benin a Jamus za su zama na Najeriya. Wannan wani aiki ne mai matukar muhimmanci. Tagulla biyu na Benin suka shiga hannun Najeriya a wannan Juma'a. Daga ciki dai akwai wani farantin agaji mai suna "Sarki mai hakimai hudu" wanda ya taba kasancewa a bangon fadar masarautar Benin. Kasancewar wadannan kayan tarihi a Jamus alama ce ta ganin cewa ana kallon tagulla a matsayin alamar wulakanci na mulkin mallaka saboda tarihinsu ba zai bace ba.

Jaridar Der Tagesspiegel  ta duba batun cimaka ne; inda ta ce kaddamar da yaki kan samun wadatar alkama ya zama dole ne Afirka, don samar da wadatar abinci a cikin nahiyar - tare da yin aiki da fasahar zamani mai alkinta halittun tsirrai.  Yunwa a matsayin makamin yaki: Karancin alkaluma a yanzu ya nuna halin da ake ciki na ban tsoro. A cewar hukumar yaki da yunwa ta MDD, duk da kudurorin da aka cimma a taron kungiyar G7 kan samar da abinci, mutane miliyan 811 a duniya na fuskantar barazanar yunwa, kuma kusan biliyan biyu na fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki. A lokaci guda kuma, mutane miliyan 100 na kan yin hijira. Lamarin ya fi muni a makwabciyarmu, wato Afirka a cewar shugabannin G7. A farkon watan Yunin da ya gabata ne shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka kuma shugaban kasar Senegal Macky Sall ya ce, "Afrika ba ta da wani taimako." Sall ya yi kira ga gwamnati a Kyiv da ta kawar da nakiyoyin da sojojin Ukraine suka jibge a cikin tekun  Bahr Aswad domin kariya daga hare-haren Rasha ta yadda za a iya safarar kayan abinci da ke makale.

 
Ita ma jaridar Die Welt ta yi sharhinta ne kan batun na karancin abinci, amma ta duba batun yake-yake ne. Jaridar ta ce ana kan gabar shiga tashin hankali na yunwa. Domin a yanzu Gabashin Afirka na fuskantar fari mai ban mamaki. Lamarin ya yi muni musamman inda ake rikicin yaki da na siyasa. Jama’ar yankin ta kasance tana shan ruwan kogin da ke kusa da kauyen da ke yankin Afar na kasar Habasha. Wajen na dauke da daruruwan 'yan gudun hijira da suka tsere daga yakin a yankin Tigray. 
 

Dürre und Trockenheit am Horn von Afrika
Wara mata 'yar Habasha da ke gyara abincin da MDD ta tallafa musu a watan JanairuHoto: Claire Nevill/AP Photo/picture alliance