Birtaniya: Truss ta karbi gwamnati mai cike da kalubale
September 7, 2022An dade tsawon shekaru a tarihi ba a sami firaministar da za ta fuskanci kalubale masu yawa a lokacin da ta karbi ragamar mulki kamar wannan lokaci ba. Tsadar rayuwa da tashin gwauron zabi na farashin makamashi da kuma matsaloli dabam- dabam na ma'aikatan gwamnati sune suka yi kasar dabaibayi.
Dukkan wadannan matsaloli dai sun kasance tamkar wata tsawa ce ta fadawa kasar. Sabuwar Firaministar ta Birtaniya Liz Truss tana da jan aiki a gabanta. Ga mutane kamar Fiona wata uwa 'yar Birtaniya da ke da 'ya'ya hudu wadda kuma ke zaune a arewacin London, rayuwa a yanzu babu sauki sai ta yi taka tsan-tsan wajen sayen abinci.
"Rayuwa ta yi tsada farashin komai ya tsawwala, ba ga burodi ba, ba ga madara ba, kudinsu duk sun tashi da akalla kashi 30 cikin dari, abin da kamar wuya musamman idan kana da yaya da suka kai hudu."
Sai dai kuma wani abu da ke da matukar tada hankali shi ne yadda yara za su kasance cikin dumi idan sanyin hunturun ya shigo. Fiona ta ce za su nemi yadda za su lullube kansu a gida, su kara kaya a jikinsu a lokacin sanyin maimakon kunna nau'rar dumama daki. Rayuwa a wajen Fiona tamkar yaki ne, to amma tana fargabar a wannan sanyin huturun al'amura za su iya kara yin tsanani a gare ta da kuma 'ya'yanta.
A wani asibiti da ke tsakiyar London, ma'aikata na motar daukar mara lafiya na shirin karbar aiki daga wadanda suka gabace su. A kullum haka suke kawo marasa lafiya fiye da yadda dakin Emergency na gajin gaggawa zai iya dauka. Karancin ma'aikata da karancin kudade sun kusa durkusar da komai. Wadannan kwararrun ma'aikata haka suke fama da matsaloli a asibitocin gwamnati a kowace rana.
Shi kansa Aaron yana shakka ko zai iya ci gaba da aiki tsawon lokaci a nan gaba. Wannan dai na daga cikin tarin matsaloli da suka yi wa kasar ta Birtaniya dabaibayi.