Ana binciken hatsarin jirgin kasa a Indiya
June 5, 2023Talla
Wannan hatsarin shi ne daya daga cikin manyan iftila'in da suka fadawa kasar a baya bayan nan, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane kusan 300 tare da jikkata daruruwan wasu. Tuni dai Jami'an tsaro suka kaddamar da bincike kan wannan iftila'in.
Ministan sufurin jiragen kasa Ashwnin Vaishnaw ya danganta hatsarin da samun matsalar lalacewar na'urar lantarki da jirgin ke amfani da shi.
Jami'an layin dogo da shaidu sun taru don gabatar da shaida ga wani binciken na kwanki biyu da suka gabata, karkashin jagorancin kwamishinan kula da lafiyar jiragen kasa a jihar West Bengal mai tazarar kilomita 120 daga wurin da hatsarin ya faru.