Jirgin saman Fasransa ya yi sabkar gaggawa a Mombasa
December 20, 2015Talla
Wani jirgin jigilar fasinja na kamfanin Air France ya yi saukar gaggawa a daran Asabar washe garin wannan Lahadi a birnin Mombasa na kasar Kenya bayan da aka gano wani kunshi da ba a yarda da shi ba a cikin jirgin wanda ya taso daga tsibirin Moritiyas zuwa birnin Paris dauke da fasinjoji 459.Hukumar 'yan sandar kasar ta Kenya wacce ta bayyana wannan labari ta ce jirgin ya nemi izinin saukar gaggawa bayan da aka gano wani kunshi a cikin bandakinsa da ake zaton Bam ne.
Tuni dai aka tura da jami'an hukumar 'yan sanda masu yaki da aiyyukan ta'addanci kwararru a fannin kwance domin binciken kunshin dama jirgin baki daya.