Joe Biden da Ji Xinping na tattaunawa
November 16, 2021Makasudin wannan ganawa shi ne daidaita tsamin dangantaka da kasashen Amirka da Chaina ke fuskanta a baya-bayan nan. Batun tsaro da kasuwanci na daga cikin batutuwan da suke gaban shugabannin biyu a wannan zama.
Wahington karkashin jagorancin Biden na zargin Chaina da take hakkin al'umma da ke zama tsiraru Musulmai 'yan kabilar Uyghurs gami da murkushe masu neman 'yancin yankin Hong Kong. Dama yadda a baya-bayan nan Biden ya sha alwashin taimaka wa tsibirin Taiwan daga barazanar mamayar Chaina.
Shugabannin kasashen biyu sun bukaci kyautata dangantakar diplomasiyyar da ke tsakaninsu, inda Biden ya ce kar su bari ta rikide zuwa rikici. Shi kuwa Xi Jinping ya ce akwai bukatar kasashen biyu su inganta musayar yau a tsakaninsu gami da fuskantar kalubalen da duniya ke fama da shi.