1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

John Dramani Mahama ya lashe zaben Ghana

December 10, 2012

Shugaba John Dramani Mahama na Ghana ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi na Juma'ar da ta gabata a takararsa da Nana Akufo-Ado na jam'iyyar adawa ta NPP.

https://p.dw.com/p/16yxS
Hoto: Getty Images

Da ya ke bayyana sakamakon zaben, shugaban hukumar zaben kasar Ghana Dr. Kojo Afari Gyan ya ce John Dramni Mahaman na jam'iyyar NDC ya samu kuri'u miliyan biyar da dubu dari biyar da saba'in da hudu da dari bakwai da sittin da daya yayin da Nana Akufo-Ado na jam'iyyar NPP ya samu kuri'u miliyan biyar da dubu dari biyu da arba'in da takwas da dari takwas da casa'in da takwas.

Bisa ga wannan alkaluma da aka fitar dai kamar yadda hukumar zaben ta ambata shugaba John Dramani Mahama ya kasance sabon zababben shugabar kasar ta Ghana, to sai dai 'yan adawa na tababa da  wannan sakamako hasali ma ba su hallarci wajen bayyana sakamakon zaben ba domin a cewarsu jam'iyya mai mulki ta hada kai da hukumar zabe wajen tafka magudi.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Halima Balaraba Abbas