'Yan majalisun dokokin Tarayyar Najeriya sun fara wani gagarumin yunkuri na tsige shugaban kasar Goodluck Ebele Jonathan, bisa zargin sa da karya ka'idojin tsarin mulki a lokuta da dama, yayin da a hannu guda kuma aka yi uwar watse a majalisar wakilai da Sifeto janar na 'yan sandan kasar Suleiman Abba da ya bayyana agabanta.